logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijer ya gana da ministan tsaron kasar

2022-03-25 10:38:52 CRI

Jiya Alhamis, jakadan kasar Sin dake kasar Nijer Jiang Feng, ya gana da ministan tsaron kasar Alkassoum Indattou, inda suka yi musayar ra’ayi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar harkokin soja da sauransu.

Jiang Feng ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Nijer suna da zumunci mai zurfi, kuma cikin ’yan shekarun nan, kasashen biyu na ci gaba da karfafa fahimtar siyasa a tsakaninsu, da kuma habaka hadin gwiwa bisa fannoni daban daban. Ya kara da cewa, Sin tana godiya ga kasar Nijer kan yadda take kare tsaron kamfanoni da ma’aikata Sinawa, wadanda suke tafiyar da manyan shirye-shirye a kasar. Har ila yau, kasar Sin tana fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Nijer kan ayyukan soja, domin daga dangantakar dake tsakanin sojojin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare kuma, Alkassoum Indattou ya ce, kasar Sin da kasar Nijer na da kyakkywar dangantaka, sun kuma cimma sakamako da dama bisa kyakkyawar hadin gwiwar dake tsakaninsu. Ya ce Nijer tana godiya matuka dangane da goyon baya da taimakon da kasar Sin take baiwa rundunar sojanta. Kuma, kasar tana son ci gaba da karfafa mu’amalar ayyukan soja a tsakanin kasashen biyu, domin zurfafa hadin gwiwarsu kamar yadda ake fatan. (Maryam)