logo

HAUSA

Hare-haren ’yan ta’adda sun ragu da kaso 7 a Mali

2022-03-25 10:43:27 CMG Hausa

Kakakin MDD Stepphane Dujarric, ya ce an bayar da rahoton fararen hula 886 da a cikinsu, wasu suka mutu, wasu suka jikkata, yayin da aka sace wasu ko kuma suka bata, a rabi na biyu na shekarar 2021 a kasar Mali, wanda ya nuna raguwar irin wadannan ayyuka da kaso 7, idan aka kwatanta da farkon watanni 6 da suka gabaci lokacin.

Da yake bayyana hakan a jiya Alhamis, Stephane Dujarric ya ce duk da raguwar, mutanen da hare-haren ya shafa na da yawa. Yana mai cewa, akwai yuwuwar ba a samu rahoton wasu daga cikinsu ba.

Yanayi ya nuna cewa, kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi ne suka fi aikata laifukan kan fararen hula, yayin da rikicin tsageru da na sauran kungiyoyin kare kai tsakanin al’ummomi, suka ragu. Baya ga wadannan, rahoton ya kuma bayyana laifukan take dokoki daga dakarun tsaron kasar ta Mali.

A cewar Stephane Dujarric, yankin tsakiyar kasar ne ya fi fama da rikici. Kana, yanzu haka, ana gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru a rubu’in farkon bana. (Fa’iza Mustapha)