logo

HAUSA

Shekaru 23 da harin bam da NATO ta gudanar Sin da Serbia ba za su mance ba

2022-03-25 20:39:08 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce la’akari da mummunan laifin da kungiyar tsaro ta NATO ta aikata, na kisan fararen hula a kasashen Serbia, da Iraki, da Afghanistan, Amurka da NATO ba su cancanci nunawa wata kasa yatsa ba, idan dai ana batu ne na kare hakkin bil Adama.

Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na yau Juma’a, ya ce al’ummar Serbia, da na Sin, da ma na sauran sassan duniya, ba za su taba mancewa da harin bama-bamai da kungiyar NATO ta kaddamar a Serbia a shekarar 1999 ba.

Ya ce, ba tare da neman amincewar MDD ba, a ranar 24 ga watan Maris na shekarar 1999, Amurka ta jagoranci NATO, wajen kaddamar da hare-hare kan Yugoslavia, matakin da ya yi matukar keta ka’idojin kasa da kasa, da tsarin cudanyar kasashen duniya. Cikin kwanaki 78 da aukuwar harin, an hallaka dubban fararen hula, ciki har da wasu Sinawa ‘yan jarida su uku, tare da lalata cibiyoyin kula da lafiya, da makarantu, da wuraren tarihi na kasar.

Wang ya kara da cewa, a matsayin ta na ribar cacar baka, kungiyar NATO ba ta taba karawa duniya wata fa’ida ta zaman lafiya ba, don haka duk mai kaunar zaman lafiya, ba zai yi na’am da fadadar kungiyar NATO ba.  (Saminu)