logo

HAUSA

‘Yan sama jannatin Shenzhou-13 na shirin dawowa doron duniya

2022-03-25 20:49:03 CMG Hausa

 

‘Yan sama jannatin dake cikin kumbon Shenzhou-13 na kasar Sin, na shirin dawowa gida nan da ‘yan kwanaki, bayan shafe watanni 6 suna gudanar da ayyukan da aka tsara a tashar sararin samaniya.

‘Yan sama jannatin Sinawa, Wang Yaping, da Zhai Zhigang da Ye Guangfu, sun gabatar da ajin koyar da kimiyya na Tiangong a karo na biyu, da yammacin ranar Laraba.

Cikin sama da watanni 5 da suka shafe suna aiki a sararin samaniya, ‘yan sama jannatin sun cimma nasarar gudanar da jerin wasu ayyuka, ciki har da ayyuka 2 a wajen kumbon su, sun kuma sauke kayayyakin dake cikin kumbon Tianzhou-2 zuwa tashar bincike ta Tianhe, ta hanyar amfani da mutum-mutumin inji.

Kari kan hakan, sun kuma gudanar da bincike game da ingancin fasahohin gudanar da rayuwa, da gwajin dukkanin abubuwan da ake bukata, domin tsawaita rayuwar bil Adama a tashar binciken da kasar Sin ke ginawa a samaniya.

Kamar yadda aka tsara, ‘yan sama jannatin za su dawo doron duniya ne, bayan kusan kwanaki 180, wato wajen tsakiyar watan Afirilun dake take ke nan.   (Saminu)