logo

HAUSA

Shugaba Xi ya zanta da shugaban Koriya ta Kudu mai jiran gado

2022-03-25 20:25:09 CMG Hausa

 

Da yammacin Juma’ar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da shugaban Koriya ta Kudu mai jiran gado Yoon Suk-yeol. Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya ce a bana za a cika shekaru 30, da kulla huldar diflomasiyya tsakanin sassan biyu, don haka ya kamata kasashen su yi amfani da wannan dama wajen karfafa mutunta juna, da yarda da juna ta fuskar siyasa, da inganta musayar abota tsakanin su, da bunkasa ci gaban su bisa daidaito a tsawon lokaci.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, kasar sa a shirye take ta yi aiki tare da Koriya ta Kudu, wajen karfafa hadin gwiwa a matakin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, tare da yin aiki tukuru, don tabbatar da daidaito da ingancin tsarin samar da hajoji na duniya.   (Saminu)