logo

HAUSA

An gano sassan jirgin da ya yi hadari a kudancin kasar Sin

2022-03-24 20:34:44 CMG Hausa

 

Shugaban ofishin dake lura da tsaron sufurin jiragen sama na hukumar kula da harkokin jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin Zhu Tao, ya ce an gano wasu tarkacen jirgin saman nan da ya yi hadari a jihar Guangxi, ta kudancin kasar Sin.

Zhu wanda ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a Alhamis din nan, ya ce an gano daidai wurin da jirgin ya fadi, kuma sassan jirgin sun tarwatse ne a fadin wurin da bai wuce mita 30 daga inda hadarin ya auku ba. Kana wasu sassan nasa sun fada zurfin da ya kai mita 20 daga wurin.

Ya zuwa karfe 4 na yammacin Alhamis ranar 24 ga wata, an tattaro sassa 183 na tarkacen jirgin, kana an tsinto sassan gawawwakin wasu fasinjojin dake cikin jirgin, da wasu kaya 21 na wadanda ke cikin jirgin, tuni kuma aka mika su ga tawagar masu bincike.

A ranar Litinin ne dai jirgin saman mai dauke da fasinjoji 132, ya fadi a kusa da gundumar Tengxian dake jihar Guangxi. Kuma kawo yanzu ba a samu ko da mutum guda da ya tsira daga hadarin ba. Sai dai an gano akwatin nadar bayanai guda daya daga tarkacen jirgin.   (Saminu)