logo

HAUSA

Wang Yi Ya Sake Jaddada Matsayar Kasar Sin Game Da Tallafawa Batun Falasdinawa

2022-03-24 20:25:20 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan harkokin wajen al’ummar Falasdinawa Riyad al-Maliki a jiya Laraba, a gefen taro na 48, na ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar OIC, wanda ke gudana a birnin Islamabad na kasar Pakistan.

Yayin zantawar tasu, jami’an biyu sun zurfafa tattaunawa game da hadin kan kasashen su, kuma Wang Yi ya sake jaddada matsayar kasar Sin, ta ci gaba da goyon bayan al’ummar Falasdinawa.

Wang ya ce, Sin ta amince da kiran da kungiyar kasashe musulmi ta OIC ta yi, game da batun Falasdinawa, yana mai cewa, bai kamata a nuna musu wariya, ko a manta da su ba. Kaza lika bai kamata a ci gaba da nuna musu rashin adalci na sama da shekaru 50 ba.

Wang ya kara da yin kira ga sassan kasa da kasa, da su yi watsi da halin ko in kula da kasashe yammacin duniya ke nunawa batun Falasdinawa, yana mai cewa, Sin za ta ci gaba da kasancewa tare da Falasdinawa.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen al’ummar Falasdinu ya godewa kasar Sin, bisa yadda a ko da yaushe take goyon bayan gaskiya da adalci, don gane da batun Falasdinu, da kuma yadda take mara baya ga manufofin saukaka halin jin kai da Falasdinawa ke fuskanta.

Ya kuma yi fatan dorewar goyon bayan Sin, game da matakan shawo kan kalubalen da Falasdinawa ke fuskanta, tare da kaiwa ga cimma nasarar wanzar da zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya.   (Saminu)