logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci Amurka da ta amsa tambayoyi game da dakunanta na gwaje-gwajen kwayoyin cuta dake fadin duniya

2022-03-24 20:41:53 CRI

Game da wasu dakunan gwaje-gwajen kwayoyin cututtuka masu nasaba da ayyukan soji da Amurka ke daukar nauyi a kasar Ukraine, da ma irinsu dake sauran sassan duniya, a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya kalubalanci Amurka da ta amsa tambayoyi game da batun cikin hanzari, tare da dakatar da haifar da cikas, ga binciken yarjejeniyar hana yin amfani da makamai masu alaka da miyagun cututtuka.

Wang Wenbin ya ce, a kwanakin baya, sassan kasa da kasa sun tattauna, tare da gabatar da tambayoyi, kan batun dakin gwajin miyagun cututtuka na kasar Ukraine wanda kasar Amurka ta kafa.

To sai dai kuma abun bakin ciki shi ne kalaman Amurka kan batun na cike da kurakurai da dama, kuma bangarori daban daban sun nuna shakku game da hakan. Ko shakka babu, bai dace Amurka ta yi shiru, ko ta ba da labarai marasa tushe kan wannan batu ba. (Zainab)