logo

HAUSA

An gano daya daga cikin akwatunan nadar bayanan jirgin saman kasar Sin da ya yi hatsari

2022-03-24 10:54:05 CMG Hausa

Da yammacin jiya ne, aka yi nasarar gano daya daga cikin akwatunan nadar bayanan jirgin saman fasinja na kamfanin China Eastern Airlines, da ya yi hadari ranar Litinin a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta dake yankin kudancin kasar Sin.

Shugaban cibiyar binciken hadurran jiragen sama na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin, Mao Yanfeng ne ya sanar da hakan, a wani taron manema labarai da aka kira a yammacin jiyan.

Mao ya ce, akwatin ya lalace matuka, kuma tawagar binciken na kara tabbatar da ko na'urar nadar bayanai na jirgin ne ko kuma na'urar nadar muryar abubuwan dake faruwa a dakin matuka jirgin.

Ruwan sama ya kawo tsaiko ga aikin ceto da bincike a ranar Laraba. Yanzu haka, ana ci gaba gaba da neman mutane 132 da ke cikin jirgin, da kuma daya akwatin nadar bayan jirgin. (Ibrahim)