logo

HAUSA

Ministocin wajen Sin da Nijar sun gana kan alakar dake tsakaninsu da tsaron yankin

2022-03-24 13:43:26 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, jiya Laraba ya gana da ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijar Hassoumi Massaoudou, a gefen taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi karo na 48 da aka gudanar a Islamabad, babban birnin kasar Pakistan. 

Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Nijar sun nuna amincewa da juna da abokantaka, kuma a ko da yaushe, suna goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi muhimman moriyarsu.

A nasa bangaren, Massaoudou ya ce shirin raya kasa da kasa da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, yana da hangen nesa, kuma yana da cikakken goyon bayan Nijar.

Ministan harkokin wajen na Nijar, ya kuma gabatar da batun yanayin tsaro a yankin Sahel.

Da yake mayar da martani, Wang Yi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan yadda Nijar ke kara karfin tsaro a yankin Sahel.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta samar da karin albarkatu, da hadin gwiwa mai karfi, ta hanyar karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta yadda za a tallafawa kasashen Afirka, wajen samun ci gaba tare. (Ibrahim)