logo

HAUSA

Peng Liyuan Ta Gabatar Da Jawabi Albarkacin Ranar Tarin Fuka Ta Duniya

2022-03-24 21:06:41 CMG Hausa

Uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, kuma jakadiyar fatan alheri ta hukumar lafiya ta duniya WHO game da yaki da cutar tarin fuka da HIV/AIDS, ta gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin taron ranar tarin fuka ta duniya ta bana.

Cikin jawabin nata a yau Alhamis, Peng ta ce cikin shekarun baya-bayan nan, albarkacin ayyukan wayar da kai na WHO, da hadin gwiwar sassan kasa da kasa, an cimma manyan nasarori a fannin kandagarki da shawo kan cutar tarin fuka ko TB. A bangarenta kuma, gwamnatin Sin na dora babban muhimmanci ga ayyukan yaki da cutar, ta hanyar yin gwaji kyauta, da baiwa masu fama da cutar magunguna, inda kaso 90 bisa dari na masu fama da cutar ke samun cikakkiyar jinya.

Peng Liyuan ta ce, duk da cewa an cimma nasarori sosai wajen kandagarki da shawo kan cutar, har yanzu TB na kasancewa babban kalubalen kiwon lafiyar duniya. Kaza lika bullar annobar COVID-19 ya sake ta’azzara yanayin yakin da ake yi da cutar TB.

Don haka ta yi kira da a hada hannu, wajen daukar hakikanin matakai na cimma nasarar kudurorin ci gaba mai dorewa na MDD nan da shekarar 2030 kamar yadda aka tsara, da gina al’ummar duniya mai koshin lafiya.  (Saminu)