logo

HAUSA

Kwamitin Sulhu ya gaza zartas da kuduri kan yanayin jin kai a Ukraine

2022-03-24 10:30:02 CMGHausa

Kwamitin sulhun MDD mai mambobi 15, jiya Laraba ya kasa zartas da wani kuduri kan halin da ake ciki a kasar Ukraine.

Membobi biyu, wato kasasahen Rasha da Sin sun kada kuri'ar amincewa da wannan kudiri, yayin da wasu 13 suka ki kada kuri'a. Sai dai kuma, an yi watsi da kudurin da Rasha ta gabatar.

Kafin kudirin kwamitin sulhun ya samu amincewa, ana bukatar a kalla kuri'u tara na goyon baya daga kasashe mambobin kwamitin 15, sannan dole ko Rasha, da Sin, da Birtaniya, da Faransa, da kuma Amurka dukkansu su amince da shi.

Daftarin kudurin na kasar Rasha, ya bayyana matukar damuwa kan rahotannin da ke cewa, an kashe fararen hula da kuma tabarbarewar al'amuran jin kai a Ukraine da kewaye, gami da karuwar 'yan gudun hijira. Har ila yau, kudirin ya yi kira da a kare fararen hula, ciki har da ma'aikatan jin kai da likitoci, da mutunta dokokin kasa da kasa, da kare fararen hula da muhimman ababen more rayuwa, da kwashe dukkan fararen hula cikin tsaro, da ba da damar kai agaji jin kai a kasar Ukraine. (Ibrahim Yaya)