logo

HAUSA

Wayoyin kamfanin Sin sun yi fice a kasuwannin Afrika a rubu’i na 4

2022-03-24 11:23:36 CMG Hausa

Nau’o’in wayoyin hannu na zamani wanda kamfanin Transsion Holdings, na kasar Sin ke kerawa, sun samu matukar karbuwa a kasuwannin wayoyin hannu na zamani na Afrika a rubu’i na hudu na shekarar 2021, inda adadin ya bunkasa da kashi 47.9 bisa 100, kamar yadda rahoton wani kamfanin kasa da kasa ya fitar a baya bayan nan.

Alkaluman da kamfanin na International Data Corporation (IDC) ya fitar ya nuna cewa, kamfanin Transsion, wanda ke kera wayoyin Tecno, Infinix, da Itel, ya sha gaban kamfanonin Samsung da Xiaomi (da kuma Poco) da kashi 19.6 da kuma kashi 7.1 bisa 100.

Taher Abdel-Hameed, babban mai sharhi kan bincike na kamfanin IDC ya ce, karancin wayoyin hannu a kasuwannin duniya, da matsin lambar tsadar farashi, da ingantattun gilasan fuskokin wayoyin, da kuma ingancinsu, na daga cikin dalilan da suka sanya tsadar farashin wayoyin hannu na zamani.

IDC ya ce, a shekarar 2022 yana sa ran kasuwar wayoyin hannu ta zamani ta Afrika za ta bunkasa da kashi 3.8 bisa 100 a bisa na makamancin lokacin bara. (Ahmad)