logo

HAUSA

An sake yin nasarar ba da darasi daga cibiyar binciken sararin samaniyar kasar Sin

2022-03-24 10:11:30 CRI

Jiya ne, aka gudanar da aikin ba da darasi karo na biyu daga cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Sin wato Tiangong, inda ‘yan sama jannati guda uku da suka hada Zhai Zhigang da Wang Yaping da kuma Ye Guangfu suka koyawa yara ilimin kimiyya dake shafar ayyukan sararin samaniya, inda suka nuna wa yara wasu na’urorin nazari da yanayin da suke rayuwa a cibiyar.

Darektan cibiyar raya fasahohin sararin samaniya ta cibiyar kimiyya ta kasar Sin Zhang Wei ya fayyace cewa, nan gaba za a ci gaba da gudanar da aikin ba da darasi a cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta hanyoyi daban daban, yana mai cewa,

“Hakika mun fi mai da hankali kan sha’awar da daliban makarantar midil da ta firamare suke da ita kan ilmin kimiyya, ta yadda matasan kasar Sin za su shiga aikin nazarin kimiyya a nan gaba, saboda muna ganin cewa, idan kasa tana son samun ci gaba, dole ne ta kara habaka aikin nazarin kimiyya, don haka akwai bukatar matasa su kara shiga aikin.”(Jamila)