logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya kaddamar da kamfanin taki na dala biliyan 2.5

2022-03-23 10:32:44 CMG Hausa

A ranar Talata shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya bude kamfanin samar da takin zamani wanda ya lashe kudi dala biliyan 2.5 a yankin masana’antu na Lekki dake birnin Legas.

A jawabin da ya gabatar a bikin bude kamfanin, shugaban Najeriyar ya ce, kamfanin takin zamanin na Dangote zai bunkasa kasuwar musayar kudaden waje da kuma bunkasar tattalin arzikin kasar.

Shugaban ya kara da cewa, ana sa ran kamfanin zai taimaka wajen cimma muradun gwammatin kasar na samun dogaro da kanta a fannin wadata kasar da abinci.

A cewar shugaba Buhari, sabon kamfanin zai taimaka wajen ragewa kasar dogaro da shigo da takin zamani daga kasashen waje, kuma zai samar da ayyukan yi, da bunkasa kasuwar musayar kudaden waje, da kuma ci gaban tattalin arzikin kasar.

Shugaban kasar ya bayyana kwarin gwiwa cewa, jarin kamfanin zai kasance tamkar na rukunin kamfanonin siminti na Dangote, wanda ya shahara matuka a Najeriya har ma da nahiyar Afrika.

A nasa bangaren, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce, kamfanin zai taimaka matuka wajen rage girman matsalar rashin ayyukan yi, da rage adadin matasa masu zaman kashe wando, ta hanyar samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye da wadanda ba na kai tsaye ba. (Ahmad)