logo

HAUSA

Duniyar Da Babu Zaman Lafiya Na Bukatar Sake Fuskantar Hanyoyin Zaman Tare Tsakanin Kasa Da Kasa

2022-03-23 11:10:07 cri

A ranar 23 ga watan Maris na shekarar 2013 ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a cibiyar huldar kasa da kasa ta Moscow, mai taken "Tsarin zamani, da inganta zaman lafiya da ci gaban duniya", inda ya bayyana cewa, "ya kamata dukkan kasashen duniya su hada kai don bullo da wani sabon nau'in alakar kasa da kasa, wanda ke mayar da hankali kan samun nasara tare ta hanyar hadin gwiwa." Wannan dai ita ce ziyarar farko da Xi Jinping ya kai zuwa ketare, tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Sin, kuma wannan shi ne karo na farko da aka gabatar da ra’ayin "Sabon Nau’in Alakar Kasa Da Kasa". Tun daga wannan lokacin, an sha bayyana "Sabon Nau’in Alakar Kasa Da Kasa " a tarukan kasa da kasa, hakan ya zama matsayin da kasar Sin ke dauka da babbar ka'idar da take bi wajen raya dangantakar kasa da kasa.

A ranar 21 ga watan Satumban shekarar 2021, lokacin da Xi Jinping ya halarci babbar muhawarar babban taron MDD karo na 76 ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing, ya sake jaddada cewa, dole ne mu karfafa hadin kai, da aiwatar da ra’ayin dangantakar kasa da kasa ta mutunta juna da samun nasara tare.

“Nasarar da wata kasa ta samu, ba ya nufin dole wata kasa ta gaza ba, duniya tana iya ba da cikakkiyar damar samun ci gaban dukkan kasashe. Dole ne mu tsaya kan tattaunawa maimakon adawa da juna, da juriya maimakon wariya, da gina sabon nau'in huldar kasa da kasa da ke mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwar cin nasara tare, da fadada fannonin samun moriyar juna.”  (Mai fassara: Bilkisu Xin)