logo

HAUSA

Xi Jinping ya mika wasikar murnar gudanar da taron kara wa juna sani a tsakanin JKS da jam’iyyar Kwaminis ta Cuba

2022-03-23 21:41:10 CRI

A yau Laraba ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika wasikar murnar gudanar da taron kara wa juna sani, a tsakanin JKS, da jam’iyyar Kwaminis ta Cuba karo na hudu.

A cikin wasikar, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, JKS da jam’iyyar Kwaminis ta Cuba, su ne cibiyoyin shugabancin sha’anin raya tsarin gurguzu na Sin da na Cuba. Ya ce bayan da aka gudanar da taron wakilan JKS karo na 18, JKS ta jagoranci jama’ar kasar Sin, wajen samun nasarori, a manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida, da kuma zamanintar da kasa mai tsarin gurguzu, don haka Sin ta shiga sabon lokaci na raya tsarin gurguzu mai alamar kasar Sin.

A gun taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta Cuba karo na 8, an gabatar da shirye-shiryen raya jam’iyyar da kasar Cuba, a yanzu da kuma nan gaba, don tsara taswirar raya kasar Cuba mai wadata, da demokuradiyya, da samun bunkasuwa mai dorewa.

Yayin da ake tinkarar sabon kalubale, taron kara wa juna sani a tsakanin JKS, da jam’iyyar Kwaminis ta Cuba ya dace da yanayin, kuma yana da babbar ma’ana wajen neman hanyar samun bunkasuwa, mai dacewa da kasashen biyu bisa tsarin gurguzu. (Zainab)