logo

HAUSA

Sin: Batun Taiwan ya sabawa halin da ake ciki a Ukraine

2022-03-23 20:40:35 CMG Hausa

A yau Laraba ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jaddada matsayar kasar Sin don gane da yankin Taiwan, yana mai cewa, batun Taiwan ko alama ya sha bamban da na Ukraine.

Wang Wenbin, ya yi tsokacin ne yayin da aka yi masa tambaya game da zantawar da jagorar yankin na Taiwan Tsai Ing-wen ta yi ta wayar tarho, da tsohon firaministan Japan Shinzo Abe a jiya Talata, inda cikin abubuwan da suka tattauna, aka ruwaito su suna musayar yawu game da halin da ake ciki a Ukraine, da batun wanzar da zaman lafiya a shiyyar Asiya da tekun Pacific.

Da yake fashin baki game da kasancewar Taiwan bangare na Sin da ba zai yiwu a balle shi ba, Wang ya ce babu ko da ma wata kalma, mai kama da shugaban kasar Taiwan.

Kuma kasar Sin na adawa da matakin duk wata kasa da ta kulla huldar diflomasiyya da Taiwan dake yin wata cudanya, ko kulla wata yarjejeniya, ko musaya da Taiwan. Kaza lika Sin na adawa da duk wani yunkuri na kulla kawance da Taiwan, ta fuskar amincewa da wasu kudurori a hukumance, wannan kuma matsaya ta Sin, da tun tuni kowa ya san da ita.

Daga nan sai Wang ya nuna damuwa, game da yadda wasu ‘yan siyasan Japan ke hada kai a zahiri da masu rajin ballewar Taiwan, matakin da ko alama Sin ba za ta taba amincewa da shi ba, ta kuma gabatar da korafin hakan ga mahukuntan Japan.  (Saminu)