logo

HAUSA

Sin: Ba Wata Kasa Cikin Mambobin G20 Da Ke Da Ikon Korar Rasha

2022-03-23 20:21:07 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Rasha muhimmiyar mamba ce a kungiyar G20, kuma ba wata mambar kungiyar dake da ikon korar ta daga G20.

Wang Wenbin, ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa, dangane da tunanin Amurka da wasu kawayenta na yammacin duniya, cewa wai suna duba yiwuwar ci gaba da kasancewar Rasha cikin kungiyar ta G20.

Wang ya ce, G20 muhimmin dandali ne, na hadin gwiwar raya tattalin arzikin sassan kasa da kasa, wanda ya hallara manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. Ya ce, a wannan gaba da duniya ke fama da yaki da annobar COVID-19, ake kuma hankoron farfadowar tattalin arziki dake fuskantar rauni, kungiyar G20 na da muhimmin nauyi na jagorantar yakin da ake yi da cutar COVID-19, da kara kyautata jagorancin tattalin arziki, da ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya sannu a hankali.

Wang ya kara da cewa, kamata ya yi kungiyar G20 ta aiwatar da manufofi na ainihin cudanyar dukkanin sassa, da karfafa mara baya ga juna, da hadin gwiwa, tare da aiki tare, wajen shawo kan manyan kalubalen tattalin arziki, da na hada hadar kudi, da ci gaba mai dorewa.  (Saminu)