logo

HAUSA

Zimbabwe ta bunkasa fannin yawon bude ido duk da tasirin COVID-19

2022-03-23 11:27:13 CMG Hausa

Fannin yawon bude ido na kasar Zimbabwe ya samu bunkasuwa daga dala miliyan 86 a shekarar 2020, zuwa dala miliyan 142 a shekarar da ta gabata, ci gaban ya biyo bayan matakan da gwamnatin kasar ta dauka ne na bunkasa zuba jari don farfado da fannin.

Ministar yada labarai ta kasar, Monica Mutsvangwa, ta bayyanawa taron manema labarai cewa, fannin yawon bude idon ya gamu da mummunan koma baya sakamakon barkewar annobar COVID-19, a tsawon shekaru biyun da suka gabata, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa guraben ayyukan  yi kimanin 9,000, da rufe bangarorin aiki kimanin 37 a kasar.

Monica ta ce, gwamnatin kasar ta aiwatar da wasu shirye-shiryen farfadowa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar a shekarar 2020, inda kasar ke da burin bunkasa kamfanonin yawon bude ido zuwa dala biliyan 5 nan da shekarar 2025.

Sannan kuma, Zimbabwe ta sha alwashin yiwa kashi 70 bisa 100 na mutanen kasar riga-kafin annobar COVID-19 ya zuwa karshen watan Yuli, bayan da kasar ta kaddamar da gagarumin shirin allurar riga-kafin a wannan mako.

Kawo yanzu, sama da kashi 35 bisa 100 na al’ummun kasar sun karbi zagaye na biyu na riga-kafin, tun bayan kaddamar da aikin riga-kafin a kasar a watan Fabrairun shekarar bara. (Ahmad)