logo

HAUSA

Sin Ta Ayyana Burin Kyautata Amfani Da Makamashi Cikin Shekaru 5 Masu Zuwa

2022-03-22 21:07:43 CMG Hausa

Mahukuntan kasar Sin sun fitar da manufar kyautata samarwa, da kuma amfani da makamashi, cikin jadawalin ayyukan raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14, wanda za a aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.

Bisa manufar, ya zuwa shekarar 2025, Sin na fatan fadada adadin makamashin da take samarwa a cikin gida, zuwa sama da tan biliyan 4.6 a bangaren kwal, kamar dai yadda kwamitin kula da ayyukan yin gyare-gyare a gida da raya kasar Sin da hukumar kula da makamashi ta kasar suka sanar da hakan.

Kaza lika an tsara daidaita yawan danyen mai da kasar za ta fitar zuwa tan miliyan 200 a duk shekara, yayin da yawan iskar gas da kasar ke samarwa zai kai sama da cubic meter biliyan 230, ya zuwa shekarar 2025.

Manufar da aka fitar, ta kuma jaddada shirin da aka tanada na fadada yawa da ingancin amfani da makamashi ta karfin iska, da na hasken rana, tare da gina makamashin nukiliya mai tsaro da kiyaye ka’idoji.

A daya bangaren kuma, an tsara bunkasa yawan makamashin kasar, yayin da Sin din ke aiwatar da matakan rage iskar carbon mai dumama yanayi da ake fitarwa kan GDPn kasar da kaso 18 bisa dari, cikin shekaru biyar din masu zuwa.  (Saminu)