logo

HAUSA

Kasar Sin ta sanya gwajin COVID-19 cikin inshorar lafiya

2022-03-22 10:59:08 CMG Hausa

Hukumar kula da inshorar lafiya ta kasar Sin, ta ce kasar ta sanya gwajin cutar COVID-19 cikin inshorar lafiya, a matsayin wani mataki na wucin gadi na yaki da annobar.

Sanarwar da hukumar ta fitar jiya, ta ce inshorar lafiya ce za ta biya kudin da aka kashe na gwajin a cibiyoyin lafiya na yankuna, yayin da mutum zai biya daga asusunsa idan ya yi a dakunan sayar da magani da ake gwajin cutar.

An kuma bukaci asusun inshorar lafiya ya rika biyan kudin sabon maganin da aka sanya cikin magungunan yaki da cutar ta COVID-19. (Fa’iza Msutapha)