logo

HAUSA

Fararen hula 25 aka kashe a harin arewa maso yammacin Najeriya

2022-03-22 10:34:47 CMG Hausa

A kalla fararen hula 25 aka kashe, kana an kona gidaje kusan 70 da safiyar ranar Lahadi, a wani harin da ’yan bindiga suka kaddamar a jihar Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda jami’in gwamnatin jihar ya bayyana.

Kashe mutanen ya yi sanadiyyar barkewar zanga-zanga a ranar Litinin, inda wasu fusatattun matasan yankin suka toshe hanyoyin mota, suka tare matafiya, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema'a da Kaura dake jihar.

Samuel Aruwan, kwamishinan al’amurran tsaro na jihar ya bayyana a wata sanarwa cewa, an dauki matakin ne domin baiwa hukumomin tsaro damar ceto rayukan al’umma da dukiyoyinsu da kuma maido da doka da oda a yankunan da lamarin ya afku. (Ahmad)