logo

HAUSA

Sin da wasu kasashe sun bayyana damuwa game da take hakkin alummu ’yan asalin wasu kasashe

2022-03-22 10:09:51 CMG Hausa

Kasar Sin da gamayyar wasu kasashen duniya sun yi kira ga hukumar kare hakkin dan adam ta MDD da ta ci gaba da dora matukar muhimmanci kan laifukan cin zarafin alummu yan asalin wasu kasashe dake zaman rayuwa a wasu kasashen domin daukar matakan da suka dace.

Da yake gabatar da sanarwar a madadin gamayyar kasashen duniyar, a wajen taron kolin hukumar kare hakkin dan adam ta MDD karo na 49, Jiang Duan, ministan tawagar wakilan kasar Sin a helkwatar MDD dake birnin Geneva, ya ce, sun yi matukar damuwa game da mummunan cin zarafi da take hakkokin bil adama da ake yiwa alummu yan asalin wasu kasashe da wasu kasashen duniya ke aikatarwa.

Ya kara da cewa, alummun yan asalin wasu kasashe, dake rayuwa a irin wadancan kasashen, suna fuskantar tsananin cin zarafi da nuna wariya, kuma ana danne hakkokinsu a harkokin yau da kullum a cikin alumma. Sannan girman matsayin muzgunawar da ake yi musu ya kara tabarbarewa ne sakamakon tasirin annobar COVID-19. (Ahmad)