logo

HAUSA

Kremlin: Lokaci bai yi ba na tattaunawa tsakanin Putin da Zelensky

2022-03-22 10:42:36 CRI

Kakakin fadar Kremlin ta Rasha, Dmitry Peskov, ya ce ya yi wuri a fara maganar tattaunawa tsakanin shugaban kasar Vladimir Putin da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky, bisa la’akari da cewa, babu wata nasara da aka samu daga tattaunawar zaman lafiya da ake yi tsakanin bangarorin 2.

A ranar Larabar da ta gabata ne, mashawarcin shugaban Ukraine Mykhailo Podolyak, ya ce akwai yiwuwar Zelensky, zai tattauna da Putin nan ba da jimawa ba. (Fa’iza Mustapha)