logo

HAUSA

Boeing China: Kwararru sun shirya don taimakawa binciken hatsarin jirgin sama na kamfanin China Eastern Airlines

2022-03-22 14:10:12 CRI

Rahotanni daga kamfanin Boeing China sun ce kamfanin na hada kai da kamfanin China Eastern Airlines, don ba shi goyon-baya game da binciken musababbin hatsarin jirgin sama kirar Boeing 737, na kamfanin China Eastern Airlines, wanda ya faru a jiya Litinin. 

A dayan bangaren kuma, Boeing China na kara tuntubar kwamitin kula da tsaron zirga-zirga na kasar Amurka, inda kwararru suka shirya tsaf don taimakawa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta kasar Sin wajen gudanar da binciken musabbabin hadarin.

Jiya Litinin da yamma ne, wani jirgin saman fasinja kirar Boeing 737 mallakar kamfanin China Eastern Airelines, mai dauke da fasinjoji 123, tare da ma’aikata 9, ya yi hatsari a kan hanyarsa daga Kunming zuwa Guangzhou. A halin yanzu ana kokarin gudanar da ayyukan ceto da binciken musabbabin faruwar hatsarin.(Murtala Zhang)