logo

HAUSA

Ba za a bukaci matafiya da suka yi cikakkun rigakafi su nuna shaidar PCR ta COVID-19 idan za su tashi daga Najeriya ba

2022-03-22 19:53:55 CMG Hausa

 

Sakataren gwamnatin Najeriya, kuma shugaban kwamitin ko ta kwana na shugaban kasa kan yaki da annobar COVID-19 Boss Mustapha, ya ce daga ranar 4 ga watan Afrilun dake tafe, ba za a sake bukatar matafiya da suka yi cikakkun alluran rigakafin cutar COVID-19, su nuna shaidar gwajin cutar na PCR, yayin da suke shirin tashi daga kasar zuwa kasashen waje ba.

Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a jiya Litinin, a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Ya ce ga matafiya masu shigowa kasar kuwa, za a rika daukar samfurin su domin yi musu gwajin gaggawa, yayin da suka iso filayen saukar jiragen sama na kasar.

Jami’in ya ce, ga matafiyan da ba su yi cikakkun rigakafin, ko wadanda kwata-kwata ba su yi ko allura daya ba, za a yi musu gwajin cutar sa’o’i 48, kafin su tashi daga filin jirgin saman kasar. Kaza lika ga masu shigowa na wannan rukuni, za su yi gwajin cutar kwanaki 2 da kwanaki 7 bayan isowar su.  (Saminu)