logo

HAUSA

Sin da kasashe musulmi na da burin zurfafa hadin gwiwa

2022-03-22 10:50:01 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kasar Sin da kasashen musulmi na da buri mai karfi na hadin gwiwa domin hadin kai da tabbatar da adalci da samun ci gaba.

Yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Pakistan, Shah Mahmood Qureshi, Wang Yi ya ce wannan ne karon farko, a matsayinsa na ministan harkokin wajen Sin da ya halarci taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen musulmi ta OIC, wanda shi ne irinsa na 48 da aka yi a birnin Islamabad.  

A cewar Wang Yi, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen musulmi, muhimmin bangare ne na hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

Da yake bayyana gagarumar dama da ka’idojin dake tattare da hadin gwiwar bangarorin biyu, Wang Yi ya ce, a shirye Sin take ta hada hannu da aminanta musulmai wajen bayar da gudunmawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya da ma ci gabansa. (Fa’iza Mustapha)