logo

HAUSA

CNN: Galibin Amurkawa na ganin kasarsu ba ta bi alkiblar da ta dace ba

2022-03-22 11:06:01 CMG Hausa

Wani rahoton kafar yada labarai ta CNN ya ruwaito cewa, galibin Amurkawa na ganin kasarsu ta dauki wata akiblar da ba ta dace ba. Rahoton ya dogara ne da wani nazari na jami’ar Monmouth.

Bisa nazarin da aka wallafa makon da ya gabata, manazarta sun bukaci Amurkawa su yi bayani game da kasar cikin kalma guda, inda 1 cikin kowanne mutum 10 da suka amsa, suka yi amfani da kalmar rabuwa ko kalmomin dake da alaka da wariya, rikici da karaya. 

1 bisa ukun wadanda suka amsa tambayar, sun yi amfani da kalamai marasa dadi wajen bayyana kasar, inda kuma kaso 73 suka bayyanata a matsayin wadda ta dauki wata bahaguwar alkibla. (Fa’iza Mustapha)