logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi bayani game da shawarwarin da aka yi a tsakanin Wang Yi da ministocin harkokin wajen kasashen Afirka uku

2022-03-21 20:30:47 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi bayani a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau, game da shawarwarin da aka yi a tsakanin memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da ministocin harkokin wajen kasashen Zambiya, da Algeriya, da Tanzania.

Kakakin ya bayyana cewa, a ganin ministocin harkokin wajen Sin da na kasashen Afirka uku, rikicin kasar Ukraine ya yi babban tasiri ga yanayin nahiyar Turai, har da ma dukkan duniya. Ya ce duniya tana kunshe kasashe da dama, ana kuma samun matsaloli da dama, amma bai kamata a manta da nahiyar Afirka, da kawo illa ga kasashen nahiyar ba.

Wang Wenbin ya kara da cewa, kasar Sin da kasashen uku, za su kara yin hadin gwiwa a fannonin yaki da cutar COVID-19, da kiwon lafiya, da raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da taimakawa bunkasa nahiyar Afirka, da sa kaimi ga raya tsarin demokuradiyya, a fannin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kara yin mu’amala kan harkokin kasa da kasa da sauransu, ta yadda za su kara sada zumunta da juna, da zurfafa hadin gwiwarsu baki daya. (Zainab)