logo

HAUSA

Tommy Xie: Sin na da kwarewar raya tattalin arziki

2022-03-21 11:14:57 CRI

Kwanan baya, shugaba mai kula da harkokin yankunan da Sinawa suke zaune na bankin OCBC na kasar Singapore Tommy Xie, ya bayyana cewa, kasar Sin tana da kwarewa wajen raya tattalin arziki, sabo da manufofi masu dacewa da gwamnatin kasar ta fidda, da ma sauran dalilai.

Ya ce, manufofin da kasar Sin ta fidda sun ba da tabbaci ga kasar wajen fuskantar kalubaloli, kamar karancin kayayyakin da ake shigowa da su. Gabanin karuwar farashin makamashi da manyan hajoji a kasashen duniya, gwamnatin kasar Sin ta fidda matakai da dama domin daidaita matsalar, lamarin da ya nuna kwarewarta wajen kare yanayin zaman karko na tattalin arzikin kasar.

Ya kara da cewa, bukatun al’umma kan sabbin makamashi yana karuwa sakamakon tashin farashin makamashi da hauhawar farashin a kasashen duniya, sannan kuma, sabbin makamashi na haifar da karin tasiri kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar, kamfanonin da abin ya shafa za su ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata a kasar Sin. (Maryam)