logo

HAUSA

Sin da sauran kasashe masu tasowa sun nuna matukar damuwa da daukar matsaya guda kan halin da yankin Turai ke ciki

2022-03-21 11:01:40 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a ranar Lahadi cewa, rikicin Ukraine yana karuwa ta yadda lamarin ya zarce batun dake shafar kasar kadai, tasirin rikikcin yana shafar duk duniya, kuma game da wannan batu, mafi yawan kasashen duniya, da suka hada da kasar Sin, da sauran kasashe masu tasowa, suna nuna damuwa matuka da kuma daukar matsaya iri daya.

Wang ya fadawa yan jaridu cewa, bayan musayar raayoyi da ministocin harkokin wajen kasashe da dama daga yankin Asiya da Afrika, ya fahimci cewa kasashe da dama, kamar kasar Sin, suna ci gaba da bibiyar halin da ake ciki game da rikicin Ukraine, kuma suna yin magana da murya guda.

Ya bayyana cewa, tun gabanin wannan lokaci, kamata ya yi bangarorin Turai su amince da bin tafarkin tabbatar da tsaro bisa hadin gwiwa, ta hanyar mutunta hakkokin tsaro na kowane bangare, su yi kokarin ingiza matakan tattaunawar sulhu don tabbatar da adalci, da kuma bin ingantaccen tsarin tabbatar da dorewa da zaman lafiya da tsaron shiyyar.

Wang ya ce, a matsayinsu na muhimman yan uwa daga kasashen Afrika, kasar Sin za ta ba da cikakken goyon baya ga kasashen Afrika domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da tallafawa Afrika don cimma nasarar farfadowar tattalin arziki, da tallafawa Afrika don kare hakkokinta da moriyarta, da kuma bayar da cikakkiyar gudunmawa don tabbatar da tsayawar Afrika da kafafunta da samun dawwamamman ci gaban nahiyar. (Ahmad)