logo

HAUSA

Shugaba Xi ya ba da umarnin aiwatar da dukkanin matakai na ceton rayuka sakamakon hadarin jirgin saman fasinja

2022-03-21 20:09:42 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da umarnin aiwatar da dukkanin matakai na ceton rayuka, bayan da wani jirgin saman fasinja mai dauke da mutane 132, ya yi hadari a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai, da yammacin yau Litinin.

Xi ya bayyana matukar kaduwa da jin labarin hadarin jirgin, na kamfanin China Eastern Airlines mai lamba MU5735.

Tuni dai ya umarci dukkanin sassan dake da ruwa da tsaki, da su gaggauta aiwatar da ayyukan jin kai, da sauran ayyukan da suka wajaba. Shugaban na Sin ya kuma umarci da a binciko musabbabin aukuwar hadarin, da karfafa matakan kariya, da kyautata tsarin aikin sufurin saman kasar, ta yadda hakan zai ba da damar gudanar da sufurin jiragen sama bisa cikakkiyar kariyar rayukan jama’a.   (Saminu)