logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da ministan harkokin watsa labaru da al’adu na kasar Nijeriya

2022-03-20 16:31:56 CMG

A kwanakin baya, jakadan Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun, ya gana da ministan harkokin watsa labaru da al’adu na kasar Nijeriya Lai Mohammed, inda bangarorin biyu suka tattauna kan hadin gwiwarsu a fannonin raya al’adu, da yawon shakatawa.

Jakada Cui ya bayyana cewa, a shekarar 2021, kasashen biyu sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kafa dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, tare da gudanar da bukukuwa da dama tare, inda suka samu nasarori da dama kan mu’amalar al’adunsu, kana yana fatan Sin da Nijeriya za su kyautata manufofinsu na samun bunkasuwa a sabuwar shekara don samun kyakkyawar makoma tare.

A nasa bangare, minista Lai ya bayyana cewa, bayan da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Nijeriya, kasashen biyu sun zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, musamman al’adu da yawon shakatawa. Kasashen biyu sun kafa cibiyoyin al’adu, da horar da kwararru kan mu’amalar al’adu, da daddale yarjejeniyar raya sha’anin yawon shakatawa da sauransu. Nijeriya tana fatan kasar Sin za ta kara zuba jari ga kasuwar yawon shakatawa ta kasar Nijeriya, da gaggauta aikin raya harkokin telebijin ta fasahar zamani a kasar Nijeriya, musamman kara yin hadin gwiwa kan fannin sinima, da taimakawa kasar Nijeriya wajen inganta fasahohin tsara sinima. (Zainab)