logo

HAUSA

An kammala gwajin tashi da saukar jiragen sama a filin jiragen sama masu daukar kayayyaki na musamman na farko na kasar Sin

2022-03-20 17:09:24 CMG

Bayan da jirgin sama samfurin Boeing 757-200 mai jigilar kayayyaki kawai ya sauka a filin jirgin sama na Huahu a birnin Ezhou a daren jiya ba tare da wata matsala ba, an gama gwajin tashi da saukar jirgin sama a filin jiragen saman Huahu, wannan ne karo na farko da aka gama aikin tashi da saukar jirgin sama mai daukar kayayyaki kawai a sabon filin jiragen sama na kasar Sin.

Aikin ya kumshi bincike kan fannonin tsarin kayyade zirga-zirgar jiragen saman, da hidimomin da aka samar a filin jiragen saman, da daidaita matsaloli cikin gaggawa da dai sauransu, yana da babbar ma’ana ga bude wannan filin jiragen sama a karshen watan Yuni yadda ya kamata.

Filin jiragen saman Huahu, shi ne filin jiragen sama na farko na tashi da saukar jiragen sama masu daukar kayayyaki kawai a nahiyar Asiya, kuma na hudu a duniya. Bayan da aka gama gina shi, shi da filin jiragen saman Tianhe na birnin Wuhan za su kasance muhimman cibiyoyin biyu na zirga-zirgar mutane da kayayyaki ta jiragen sama a lardin Hubei. (Zainab)