logo

HAUSA

Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Zambia Sun Tattauna A Anhui

2022-03-20 15:59:14 CRI

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a ranar Asabar ya tattauna da ministan harkokin wajen kasar Zambia, Stanley Kasongo Kakubo, a birnin Tunxi na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin.

Da yake maraba da Kakubo, a matsayin ministan harkokin waje na farko na kasar da ke kudu da hamadar Afrika da ya ziyarci kasar Sin tun bayan barkewar annobar COVID-19, Wang ya ce, kasar Sin tana goyon bayan zabin da kasar Zambia take da shi na neman hanyar ci gabanta wadda ta dace da yanayinta.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Zambia domin karfafa tuntubar juna, da zurfafa musayar kwarewar gwamnatocin biyu, da kyautata mu’amala da kuma fadada hadin gwiwar kasashen a fannoni daban-daban.

Kakubo, ya taya kasar Sin murnar samun nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta shekarar 2022, sannan ya yaba wa kasar Sin bisa gudunmawar da take baiwa ci gaban nahiyar Afrika cikin dogon lokaci, da kuma yadda take kiyaye dokoki da tabbatar da adalci a harkokin kasa da kasa.

Bangarorin biyu, sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan batun Ukraine. Kakubo ya yabawa kasar Sin bisa rawar da take takawa wajen kara azama kan tattaunawar zaman lafiya, da kuma rawar da take takawa cikin dogon lokacin don tabbatar da dorewar zaman lafiya.(Ahmad)