logo

HAUSA

SCMP: Za A Samu Karuwar Kayan Amfanin Gonar Afrika A Kasuwannin Sin

2022-03-20 20:21:30 CRI

Sakamakon sassaucin ka’idojin kasuwancin da hukumar kwastom ta kasar Sin ta yi wa wasu kasashen Afrika, matakin ya bayar da damar samun karuwar kayan amfanin gona daga nahiyar zuwa kasuwannin kasar Sin, kamar yadda rahoton da jaridar South China Morning Post, SCMP ta fitar.

A baya-bayan nan, kasashen Afrika ta Kudu, da Kenya da Zimbabwe, suna daga cikin kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyoyin da aka yi wa gyaran fuska, lamarin da ya ba su damar shiga kasuwannin kasar Sin.

A watan jiya, kasar Afrika ta Kudu ta sayar da kashin farko na lemon tsaminta 100,000 zuwa kasar Sin. Kasar Tanzania ta fara sayar da waken soyarta zuwa kasar Sin a shekarar 2020. An cimma makamanciyar wannan yarjejeniya don sayar da avocados, da ganyen shayi, da kofi da furanni daga kasar Kenya, da kuma kofi da waken soya daga kasar Habasha, sai naman shanu daga kasashen Namibia da Botswana, da ‘ya’yan itatuwa daga kasar Afrika ta Kudu, sai kofi daga kasar Rwanda a kasar Sin.

Kamfanin bincike da ba da shawarwarin kasuwanci na Oxford Business Group ya bayyana cikin rahotonsa na baya-bayan nan cewa, duk da irin kalubalolin da duniya ke fuskanta a tsarin kasa da kasa na samar da kaya, amma cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta samu gagarumar bunkasuwa a shekarar 2021.(Ahmad)