logo

HAUSA

Sin Ta Dau Matsaya Mafi Dacewa Game Da Batun Ukraine

2022-03-20 16:47:48 CRI

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana a jiya Asabar cewa, kasar Sin tana kan matsaya ta adalci game da batun Ukraine, kuma lokaci ne zai tabbatar cewa, ta dauki matsaya mafi dacewa a tarihi .

Wang, ya yi wannan tsokaci ne a yayin da yake jawabi ga ‘yan jaridu game da musayar kalaman da aka yi tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka kan batun Ukraine, inda suka tattauna ta kafar bidiyo a ranar 18 ga watan Maris.

Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta bayyana a fili karara game da matsayarta kan batun Ukraine. Abu mafi muhimmanci shi ne, a ko da yaushe kasar Sin burinta shi ne tabbatar kiyaye zaman lafiyar duniya.

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan manufarta na tabbatar da adalci bisa tsari na adalci ga kowane bangare kan wannan batu. Wang ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta taba yin kasa a gwiwa kan matsayarta sakamakon matsin lamba daga kowane bangare ba, kuma tana adawa da dukkan wasu zarge-zarge marasa tushe da ake yi mata.

Ya ci gaba da cewa, babban abin da ake baiwa fifiko shi ne, tilas ne dukkan bangarori masu ruwa da tsaki su yi kokarin ingiza matakan tattaunawar sulhu, da kuma gaggauta cimma daidaito a tsakanin bangarorin, da kawar da kiyaye ba tare da bata lokaci ba, da dena kashe fararen hula, kana a kawar da duk wani shinge da zai kawo cikas ga ayyukan jin kan bil Adama.

Hanya mafi dacewa ta kawo karshen rikicin ya dogara ne kan kaucewa amfani da halayyar yakin cacar baka, da kaucewa amfani da hanyoyi na yin fito-na-fito, kuma a gina ingantaccen tsarin adalci na tabbatar da tsaron shiyya-shiyya, domin samun zaman lafiya mai dorewa a nahiyar Turai, in ji minista Wang. (Ahmad)