logo

HAUSA

AU: Ana samun ci gaba a fannin ajandar dunkulewar nahiyar Afrika

2022-03-19 17:17:36 CRI

Wani sabon rahoton da Tarayyar Afrika (AU) ta wallafa, ya bayyana cewa, dunkulewar nahiyar Afrika ya zarce matsakaicin mataki, inda kungiyoyin raya tattalin arzikin yankunan nahiyar ke samun nasarori a wannan bangare.

Sabon rahoton kan dunkulewar Afrika ya nuna cewa, kungiyar EAC mai raya tattalin arzikin gabashin Afrika da takwaranta ta yammacin Afrika wato ECOWAS, da kasuwar bai daya ta gabashi da kudancin Afrika COMESA, sun taka rawar gani a fannin dunkulewar harkokin cinikayya, inda suka samu makin da ya haura kaso 75 cikin 100.

Rahoton na bana, wanda ya yi duba musamman kan zirga-zirgar mutane a matsayin jigon dunkulewar, ya nuna cewa, matsakaicin ci gaban da kungiyoyin yankuna suka samu wajen aiwatar da matakin zirga-zirgar jama’a ba tare da shinge ba na kan matsakaicin mataki na 0.68 idan aka auna tsakanin 0 zuwa 1.

Har ila yau, rahoton ya ce kungiyar ECOWAS da EAC sun yi wa wa sauran kungiyoyin yankunan zarra a fanin zirga zirgar jama’a cikin yanci, inda makin ECOWAS ya kai kaso 100 yayin da na EAC ya kai kaso 96. Makin sauran kungiyoyin raya tattalin arzikin yankunan nahiyar a wannan fanni, ya tsaya ne kan kasa da kaso 65.

A bangaren dunkulewar harkokin kudi, rahoton ya gano cewa, har yanzu dukkan kungiyoyin na gwagwarmayya. Sai dai, ya ce kungiyoyin SADC mai raya tattalin arzikin kudancin Afrika da EAC na gabashi, sun fi samun sakamako mai kyau a wannan fanni, bisa la’akari da kafuwar hukumomi masu ruwa da tsaki kamar na kula da hada-hadar kudi da kwamitin daidaita ka’idojin dunkulewar kudi.

Wata sanarwa da AU ta fitar a jiya game da sakamakon rahoton, ya jaddada cewa hadin kan yankin ingantacciyar dabara ce wajen tunkara annobar COVID-19 tare da inganta farfadowa bayan annobar, a matsayin wata hanya ta ingiza ci gaba mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)