logo

HAUSA

An gudanar da taro kan take hakkokin mutanen asalin Amurka da Canada da Australia

2022-03-19 17:29:52 CRI

Yayin zama na 49 na majalisar kare hakkokin bil adama ta MDD a Geneva, kasashen Sin da Venezuela, sun gudanar da wani taron bidiyon mai taken “Yadda Amurka da Canada da Australia suke take hakkin mutanen asalin kasashen”. Taron da ya gudana ta kafar intanet, ya samu halartar mutane sama da 150, ciki har da jami’an diflomasiyya dake Geneva da wakilan kungiyoyin da ba na gwamnati ba da masana da ‘yan jarida.

Minista Jiang Duan na zaunannen ofishin kasar Sin a MDD dake Geneva, ya gabatar rahoto mai taken “hakikanin tarihi da shaidun kisan kiyashin da Amurka ta yi wa Indiyawa” wanda ma’aikatar harkokin wajen Sin ta wallafa a baya-bayan nan, inda ya bayyana cewa, a yanzu mutanen asali na fuskantar wariya a kasashen Amurka da Canada da Australia. Yana mai cewa, ya kamata kasashen su yi duba kan kurakuran da suka tafka tare da bincike da hukunta wadanda ke da hannu cikin laifukan take hakkokin mutanen. (Fa’iza Mustapha)