logo

HAUSA

Sin: A matsayinta na wadda ta haddasa rikici tsakanin Rasha da Ukraine har yanzu Amurka tana fakewa ne da batun 'yan gudun hijira

2022-03-18 20:10:44 CRI

Mai magana da yawun fadar White House ta Amurka, Jen Psaki ta fada a baya-bayan nan cewa, Amurka na tattaunawa kan yadda za ta tallafawa 'yan gudun hijirar kasar Ukraine. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai Jumma’ar nan cewa, a matsayinta na wadda ta haddasa tare da ruruta rikicin Rasha da Ukraine, har yanzu Amurka tana fakewa ne kawai kan batun 'yan gudun hijira.

Zhao Lijian ya bayyana cewa, ya kamata bangaren Amurka ya yi tunani mai zurfi kan tushen matsalar 'yan gudun hijira a halin yanzu, da ma rawar da bangaren Amurka ya taka a rikicin Ukraine. Wane irin nauyi ya kamata bangaren Amurka ya dauka? Idan har ba zagaye biyar a jere na neman fadada kungiyar tsaro ta NATO zuwa yankin gabashi, wanda ya haifar da rashin daidaiton tsaron shiyya mai tsanani, ta yaya al'amura a Ukraine suka ci gaba a halin da ake a yau? Shin kasashen da suka yanke shawarar fafada kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabashi, sun yi tsammanin irin muwuyacin halin da 'yan gudun hijira za su shiga a yau?"

Da yake mayar da martani ga ikirarin Amurka cewa, wai kasar Sin ba ta nuna damuwa game da hasarar rayukan fararen hula a Ukraine ba. Zhao ya yi nuni da cewa, game da batun Ukraine, matsayin kasar Sin na adalci da kokarin da ta yi a bayyane yake ga kowa. Kasar Sin ta ba wa kasar Ukraine kayayyakin jin kai da ake bukata cikin gaggawa kamar abinci, da garin madarar yara, da katifu, da tabarmai dake juri damshi, yayin da ita kuma Amurka ta samar da muggan makamai.