logo

HAUSA

Yawan kudin ketare da aka zubawa kasar Sin a farkon watannin biyu na bana ya karu sosai

2022-03-18 10:34:37 CRI

Yawan kudin ketare da suka shigo kasuwar Sin ta bangaren da ba na hada-hadar kudi ba ya kai RMB Yuan biliyan 243.7, wanda ya karu da kashi 37.9% bisa na makamancin lokaci na bara, inda ya kai matsayin mafi saurin bunkasuwa tun daga watan Afrilu na shekarar 2021. Wani manazarci na ganin cewa, saurin shigowar jarin waje a cikin kasuwannin kasar Sin ya alamta cewa, Sin ta ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arzikinta, duk da annobar COVID-19 da ta ki ci ta ki cinyewa, da dai sauran matsaloli. Sin na ci gaba da jawo hankali masu zuba jari daga kasashen waje.

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya yi tsokaci a taron manema labarai da aka gudanar a jiya Alhamis cewa, yawan jarin da aka samu a farkon watannin biyu na bana ya karu, duk da wasu matsalolin da ake fuskanta. Ya ce:

“Tun daga farkon shekarar bana, tattalin arzikin Sin na samun farfadowa sannu a hankali. Ana kuma samun bunkasuwar bukatar kayayyaki, inda kasuwar sayayya ke samun farfadowa, abin da ya inganta kwarin gwiwar masu zuba jari na waje. Kungiyar kasuwanci ta Amurka da Jamus dake nan kasar Sin, ta ba da rahoto a kwanakin baya-bayan nan cewa, kamfanoni masu jarin Amurka da Jamus na da kashi 83% da 96%, sun nuna kyakkyawan fata ga kasuwannin Sin, sa’an nan kamfanonin Amurka na da kashi 66%, kana na Jamus na da kashi 71%, suna kuma shirin kara zuba jari a Sin.” (Amina Xu)