logo

HAUSA

Shugaban Afrika ta kudu: Kara kutsawar NATO zuwa gabas ne dalilin barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine

2022-03-18 10:35:44 CRI

 Jiya Alhamis, shugaban Afrika ta kudu Matamela Cyril Ramaphosa, ya ce sake kutsawar kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabashin Turai ne ya haddasa barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, kuma NATO ba ta fahimci illar da matakinta zai haifar, wanda ya hada da tayar da rikici.

A cewarsa, ko da yake wasu suna yunkurin rura wuta tsakanin Afrika ta kudu da Rasha, amma kasar ba za ta dauki duk wani mataki na yaki da Rasha ba, yana mai fatan bangarorin biyu da rikicin ya shafa, za su warware bambancin ra’ayi ta komawa teburin shawarwari, saboda tada yaki da nuna karfin tuwo ba za su yi wani amfani ba wajen warware matsaloli da ake fama da su.

Ban da wannnan kuma, ya ce ba wanda yake son ganin abin da ya faru a Ukraine. Shi ya sa ake ta fatan a ga an yi sulhu, da komawa shawarwari tsakanin bangarorin da rikici ya shafa. (Amina Xu)