logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci a yi kokarin hana tabarbarewar yanayin jin kai a Ukraine

2022-03-18 10:21:48 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin ya yi kira ga dukkan bangarorin dake da ruwa da tsaki a rikicin Ukraine da su kai zuciya nesa domin hana kara tabarbarewar yanayin gudanar da ayyukan jinkan bil adama.

A cewar Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, kasar Sin ta yi matukar damuwa game da tabarbarewar yanayin ayyukan jin kai a Ukraine, kana ta damu game da rahoton karuwar hasarar rayukan fararen hula da ’yan gudun hijira. Abin da ake bukata a halin yanzu shi ne, yin kira ga dukkan bangarori da su kai zuciya nesa, domin kaucewa kara rikicewar al’amurran ayyukan jin kai. 

Ya fadawa taron kwamitin sulhun MDD da aka gudanar kan batun ’yan gudun hijirar Ukraine cewa, kasar Sin tana goyon bayan dukkan bangarorin da batun ya shafa da su kiyaye tuntubar juna, a tabbatar da tsaro da bude kofa ga jami’an ayyukan jin kai, kana a kara bada dama ga jami’an dake ayyukan kwashe al’umma da masu bayar da tallafin jin kai.

Zhang ya ce, adadin ’yan gudun hijira da wadanda rikicin ya tilastawa barin gidajensu har yanzu yana karuwa, lamarin dake haifar da mummunan tasiri ga Ukraine da kasashe makwabta. Kasar Sin tana goyon bayan hukumomin MDD mafiya dacewa da su ci gaba da gudanar da ayyukansu, sannan ya bukaci kasa da kasa su samar da taimako ga dukkan masu bukatar agaji.

Ya ce, a baya bayan nan, wasu daga al’ummun kasashen Afrika ko kuma yankin gabas ta tsakiya, sun fuskanci wahalhalu a lokacin da ake kokarin kwashe su. Ya kamata a dauki wannan batu da matukar muhimmanci kuma a magance shi. Sannan ya kamata a baiwa dukkan ’yan gudun hijira cikakkiyar kariya karkashin dokokin ’yan gudun hijira ta kasa da kasa, ba tare da la’akari da launin fata, ko yankuna, ko kuma addini ba. (Ahmad)