logo

HAUSA

Wang Yi ya yi kira ga SCO da ta taka rawar gani a fannin warware rikicin Ukraine

2022-03-18 10:30:33 CMG Hausa

Babban dan majalissar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, da ta taka rawar gani, wajen tabbatar da zaman lafiya, da tsaro, da daidaito a matakan kasa da kasa da na shiyya shiyya, yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar yanayin rashin tabbas, sakamakon rikicin kasar Ukraine.

Wang ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin da yake zantawa da sabon babban sakataren SCO Zhang Ming a birnin Beijing. Wang ya jaddada adawarsa da sake farfado da cacar baka, da yin fito na fito tsakanin rukunonin kasashe. Yana mai cewa, daukar kebabbun matakan tsaro, da rungumar tsoffin dabarun tsaro, ba za su haifarwa kowa da da mai ido ba.

Ministan harkokin wajen na Sin, ya kuma yi kira da a yi watsi da daukar matakan kashin kai na kakkaba takunkumai ga wasu sassa. Yana mai kira da a martaba manufofi da dokokin MDD, tare da kare tsarin doka da oda da kasashen duniya suka amincewa.

A nasa bangare, Zhang Ming ya shaidawa Wang Yi cewa, SCO ta damu matuka da yanayin da ake ciki a Ukraine, tana kuma fatan za a kai ga shawo kan rikicin dake wakana, tare da dawo da yanayin zaman lafiya da tsaron duniya.  (Saminu)