logo

HAUSA

Xi ya zanta da takwaransa na Afirka ta kudu ta wayar tarho

2022-03-18 20:55:32 CRI

Yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ta wayar tarho.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, karfafa huldar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka ta Kudu, tana da matukar ma'ana ga jagorancin alakar dake tsakanin Sin da Afirka, da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Kasar Sin na son yin hadin gwiwa tare da kasar Afirka ta Kudu wajen ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani matsayi mai inganci, da kara fadada da zurfafa hadin gwiwar sassan biyu.

A nasa bangaren kuwa, shugaba Ramaphosa ya bayyana cewa, kasar Sin sahihiyar kawa ce kuma aminiyar Afirka ta Kudu da ta kasashen Afirka. Ya kuma gode wa kasar Sin bisa tsayawa tsayin daka kan adalci da taimako mai muhimmanci da take baiwa Afirka ta Kudu da kasashen Afirka don shawo kan matsalolinsu. Yana mai cewa, kasar Afirka ta Kudu tana tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana goyon bayan matsayin kasar Sin kan manyan batutuwa dake shafar yankin Tibet.

Shugabannin kasashen biyu sun kuma yi musayar ra'ayoyi kan halin da ake ciki a kasar Ukraine. Haka kuma bangarorin biyu sun amince cewa, kasashen Sin da Afirka ta Kudu, suna da matsayi kusan daya kan batun kasar Ukraine, kuma kasashe masu mulkin kansu suna da ‘yanci na bayyana matsayinsu, kuma suna goyon bayan Rasha da Ukraine wajen ci gaba da gudanar da shawarwarin zaman lafiya da warware takaddama ta hanyar tattaunawa da yin shawarwari.