logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya zanta da Biden ta kafar bidiyo

2022-03-18 22:28:58 CRI

Da daren ranar yau Jumma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta kafar bidiyo.

Xi ya ce, tun da suka yi shawarwari karo na farko ta kafar bidiyo a watan Nuwambar bara, zuwa yanzu, an samu wasu sabbin manyan sauye-sauye a fadin duniya. Zaman lafiya da samar da ci gaba, na fuskantar babban kalubale, duniya na fama da rashin kwanciyar hankali da tashe-tashen hankali. Ba ma son ganin barkewar rikici a kasar Ukraine. Abubuwa da dama sun sake shaida cewa, bai kamata a yi fito-na-fito ta fuskar soja ba a bangaren alakokin kasa da kasa, kuma yin taho-mu-gama bai dace da muradun kowane bangaren ba. Zaman lafiya da tsaro tamkar dukiya ce da ya kamata kasashen duniya su ririta. A matsayinsu na kasashe membobin dindindin a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, kana kasashe mafiya karfin tattalin arziki na farko da na biyu a duniya, ba kawai raya dangantakar Sin da Amurka bisa hanya madaidaiciya ya kamata mu yi ba, har ma akwai bukatar mu sauke nauyin dake wuyanmu, don kokarin taimakawa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Murtala Zhang)