logo

HAUSA

Wakilin Sin: A sa lura kan yadda aka kashe yaran kasar Afghanistan

2022-03-17 12:19:41 CRI

A jiya Laraba, wakilin Sin ya yi musayar ra’ayi da manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batutuwa masu alaka da yara da tashin hankali, a taro na 49 na kwamitin kare hakkin dan Adam na majalisar, inda wakilin na Sin ya yi kira ga kwamitin, da ya sa lura kan yadda wasu kasashen yammacin duniya, irinsu Amurka, da Birtaniya, da Australiya, da dai sauransu, suka aikata laifin kisan yara a kasar Afghanistan.

A cewar wakilin na Sin, matakin da za a iya dauka don kare yara daga wutar yaki, shi ne dakatarwa, da kawo karshen rikice-rikice. Saboda haka, ya kamata bangarori daban daban su nace ga musayar ra’ayi da muhawara, don tabbatar da zaman lafiya. Sai dai a nasu bangare, kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya, suna fakewa da maganar “kare tsarin dimokuradiya da hakkin dan Adam”, suna yin shisshigi cikin harkokin gida na sauran kasashe, da ta da yake-yake a kai a kai.

Cikin shekaru 20 da suka gabata, wato tun bayan da kasar Amurka ta fara kai hari ga kasar Afghanistan, har zuwa lokacin da ta janye sojojinta daga kasar, an samu yanayi na azabtar da yaran kasar Afghanistan. Ganin haka ya sa kasar Sin ta yi kira ga kwamitin kare hakkin dan Adam ta MDD, da ya dinga mai da hankali kan yadda sojojin kasashen yamma suke kashe dimbin yaran kasar Afghanistan. (Bello Wang)