logo

HAUSA

Karuwar rikici a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo na tarnaki ga ayyukan jin kai

2022-03-17 11:20:20 CRI

 

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD ya ce rikici mai muni dake ta’azzara a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, na kawo tsaiko ga ayyukan jin kai.

A cewar ofishin, ma’aikatan jin kai sun yi gargadin cewa, munanan hare-hare na kawo tsaiko a hanyoyin isa ga mutane masu bukatar taimako a yankin Beni, na Kivu ta Arewa dake gabashin kasar.

Ya kara da cewa, karuwar hare-hare ya tilastawa hukumomin jin kai dakatar da ayyukansu a yankin Kamango na Beni. Kana sama da mutane 300,000 ne suka rasa taimakon jin kai a yankunan kiwon lafiya na Kamango da Mutwanga da Oicha da Mabalako dake arewacin Kivu ta arewa.

Har ila yau, ofishin na MDD ya ce hanyoyin kai agaji na kara fuskantar kalubale. Yana mai cewa, sai hukumomi sun yi zagaye mai nisa daga kudancin kasar, a wani lokaci sai sun ratsa ta kasashen Rwanda da Uganda kafin su isa yankin Kamango. (Fa’iza Mustapha)