logo

HAUSA

ICRC: Matsalar fari na kara ta’azzara a Somalia

2022-03-17 10:58:50 CRI

 

Kwamitin ba da agajin jin kai na kasa da kasa ICRC, ya ce matsalar fari na kara ta’azzara a sassan kasar Somalia, don haka akwai bukatar daukar karin matakan gaggawa na shawo kan kalubalen.

Da yake tsokaci game da hakan a jiya Laraba, shugaban kwamitin mai aiki a Somalia Juerg Eglin, ya ce mutane da dama na barin gidajen su yayin da suke balaguro domin neman abinci da ruwan sha. Hakan ya zuwa ne bayan da farin ya hallaka amfanin gona da dabbobi, ya kuma kara zurfin wuraren samun ruwa.

Juerg Eglin, ya ce a yanzu haka, ICRC's ta fara aiwatar da wasu matakan gaggawa na ba da agaji, inda ake maida hankali ga sassan da ibtila’in ya fi shafa, da kuma wurare masu nisa. (Saminu Hassan)